Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya tabbatar da janye gayyatar da suka aike wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari don bude wasu ayyuka a Jihar.
Sai dai sabanin yadda ake ta yadawa, Ganduje ya ce matakin ba shi da alaka da zargin jifa da ihun ‘ba ma yi’ da ake zargin an yi wa Buharin a Jiharsa ta Katsina a cikin makon nan.
- Bayan zargin yi wa takararsa zagon kasa, Tinubu ya ziyarci Buhari a Daura
- Zulum ya raba wa ’yan gudun hijira sabbin takardun kudi a Borno
Tun da farko dai an tsara cewa Shugaban zai ziyarci Jihar Kano ranar Litinin domin wata ziyarar yini daya, bisa gayyatar Gwamna Ganduje.
Sai dai Gwamnan ya ce damuwar da halin da jama’a suka shiga sakamakon karatowar wa’adin daina amfani da tsoffin kudi ne ya sa suka nemi Shugaban ya dage ziyarar.
Ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da malamai da ’yan majalisa da shugabannin siyasa da kuma ’yan kasuwa a Fadar Gwamnatin Kano, inda ya ce an dauki matakin ne dpon gudun abin da ka je ya zo.
“A daidai lokacin da muke tsimayen wannan muhimmiuyar ziyarar, mun tsinci kanmu a wani yanayi da mutane ke cikin wahala sanadin canjin kudi. Dalilin ke nan da ya sa muka rubuta wasika zuwa ga Shugaba Buhari, muka roki ya dage ziyarar.
“An kuma aiko mana da amsar wasikar da muka aika. Amma mutane na cikin wani hali gaskiya.
“Babu yankuna a akasarin yankunan karkararmu, kuma yadda wadannan mutanen za su sami kudi abin damuwa ne,” in ji shi.
A cewar wata sanarwa da Sakatare Yada Labaran Gwamnan, Abba Anwar ya fitar ranar Asabar, ya ce yayin tattaunawar, mahalartansa sun amince da murya daya cewa janye gayyatar shi ne mafi alheri.
Sai dai Aminiya ta gano daga wata majiya cewa dage ziyarar ba zai rasa nasaba da abin da ya faru da Shugaban a Katsina ba.