✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar Boko Haram: Ko ya dace gwamnati ta hana mata sanya hijabi?

Bai dace a hana sa hijabi ba – Malam Abdulrahman BKK Malam Abdulrahman BKK: “Ni dai a ganina, bai dace a ce an hana mata…

Bai dace a hana sa hijabi ba – Malam Abdulrahman BKK

Malam Abdulrahman BKK: “Ni dai a ganina, bai dace a ce an hana mata sanya hijabi ba, domin kuwa shi hijabi ga mata, umurni ne daga Allah (swt), domin kuwa Shi ne ya gaya wa muminai mata cewa kada su yi fita irin ta jahiliyya. Kodayake muna ta addu’a, muna rokon Allah Ya kawo karshen wannan fitina ta ’yan Boko Haram, wadanda ke ta’addancin halaka bayin Allah. In Allah ya yarda, al’amarin ma ba zai ta’azzara ya kai ga an hana matanmu sanya hijabi ba. Musamman ma ganin yadda Allah Ya ba mu jajirtaccen Shugaban kasa, wanda ya maida hankali sosai wajen yaki da wannan ta’addanci, in Allah Ya yarda abin zai zo karshe. Muna rokon Allah Ya taimaki gwamnatin Buhari, Ya ba shi ikon gudanar da mulki mai inganci da adalci a kasarmu, yadda za a samu wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar arziki.”

Idan ya zama dole to a hana – Alhaji Aliyu Salihu

Alhaji Aliyu Salihu: “Ni dai a yadda na fahimta, yanayi shi ke sanyawa a dauki mataki kan wani al’amari. Game da yadda mata ’yan Boko Haram ke amfani da suturar hijabi suna gudanar da ta’addancin kashe bayin Allah da boma-bamai, muddin abin ya ta’azzara kuma aka ga cewa babu wata hanya da za a iya shawo kan lamarin sai ta hana mata sa hijabi, to ya dace a dauki wannan mataki na hanawa, na takaitaccen lokaci. Idan matsalar ta wuce, sai a bar mata su ci gaba da sanya hijabi. Domin a yadda abin yake gudana, wani namiji ne ma, amma sai ya sanya hijabi da kayan mata, ya yi badda-kama, ya tayar da bom. Kuma idan yana cikin hijabin nan, zai yi wuya jami’an tsaro su ganoi shi. Kuma ya kamata mu gane cewa shi kansa addinin Musulunci ya yarda da lalura, ya yarda da a yi gyara. Don haka, idan dai domin gyara za a hana sanya hijabi, domin a magance matsalar kashe-kashen al’umma, to ya dace a hana. Idan an gama gyaran, komai ya dawo daidai yadda ake so, sai a bar mata su ci gaba da amfani da suturar hijabi kamar yadda ya kamata.”

Babu laifi idan an hana nikabi – Malama Saratu

Malama Saratu dalhatu Ibrahim: “Daman rashin bin dokokin Ubangiji ne ke haifar da irin haka da kuma rashin shugaba adali, sannan kuma Musulunci abu ne mai sauki wanda Allah bai bar kamai ba sai da ya ba da hanyar warware shi. Idan har abin ya ta’azzara, to ba laifi ba ne idan aka dakatar sanya nikabi, don a shawo kan wata matsala. Hijabi da safa ne wajibi, wannan babu  lalurin da zai sa, a ce a bar sa hijabi. Amma shi nikabi, kari ne kan sunna, idan saboda a shawo kan wannan matsalar ce sai a hana shi, amma idan ba haka ba, babu dalilin da zai sa a hana a sanya nikabi.”

Nikabi ba dole ba ne – Malama Fatima

Malama Fatima Ahimad: “Ni a nawa ra’ayin, tun da nikabi ba dole ba ne, tunda muna cikin matsalar rashin natsuwa kuma abu ya kai haka, to ba laifi ba ne a dakatar da amfani da shi har sai an warware wannan matsalar. Amma shi hijabi, babu mai iya tabawa, bai kamata a yi dokar hana sanya shi ba.”

Ya dace a hana don kare lafiya- Hajiya A’isha

Hajiya A’isha Muhammad: “A ra’ayina, idan har masu kai harin nan suka ci gaba da yin amfani da hijabi ko nikabi suna kai hare-hare, to ina goyon bayan a hana sa hijabin gaba daya, don a  kare lafiyar jama’a. Allah Ya gani, lalura ce. Sai mu rika amfani da mayafai manya da za su lullube mana jiki gaba daya.”

Kamata ya yi a samo wata hanyar – Bilki Otaru

Bilki Otaru: “Ni ina ganin zai fi kyau gwamnati ta samo wata hanyar da za ta tunkari wadannan mutanen amma ba ta hanayra hana sa hijabi ba. Kasancewar mafi yawanmu mun saba da sanya hijabi, idan ka ce mu koma sanya wani kayan ba hijabi ba, a gaskiya ba zai yi mana dadi ba. Wata ma wallahi ba za ta taba iya fita waje ba tare da hijabi ba.”