✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matsahi ya kashe dan acaba saboda ya taka karensa

Wanda ake zargin ya ce ya aikata kisan ne a bisa kuskure

Wani matashi a Gombe ya kashe dan acaba ta hanyar caka masa wuka saboda dan acabar ya taka masa kare a bisa kuskure.

Matashin, wanda ake wa lakabi da Shetti ya caka awa dan acaban mai suna Saleh Babayo wuka ne saboda ya taka wa matashin karensa mai suna Dan Tawaye.

Da yake gabatar da Shetti ga manema labarai, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Gombe, Ishola Babatunde Babaita, ya ce an cafke matashin ne a Kumo bayan ya aikata kisan a ranar 28 ga watan Fabarairu, 2022.

Kwamishinan ’Yan Sanda ya ce an kai Saleh asibitin garin Kumo bayan Shetti ya caka mishi wuka, amma likita ya tabbatar cewa rai ya yi halinsa.

Ya bayyana cewa Shetti mai shekara 25 yana hannun ’yan sanda kuma da zarar sun kammala bincike za su tura shi zuwa kotu.

Lamarin dai ya faru ne a kauyen Akkoyel da ke Kumo, hedikwatar karamar hukumar Akko a Jihar Gombe.

Tsautsayi ya gitta

Shetti ya shaida wa Aminiya cewa gaske ne ya kashe Saleh dan acaba, amma ba da gangan ya kashe shi ba.

Da yake zantawa da wakilinmu a hedikwatar ’yan sanda ta Jihar Gombe, matashin ya ce tsautsayi ne ya gitta, har ya yi sanadin mutuwar dan acaban.

A cewarsa, abin ya faru ne a bayan ya je sayen wando a wani shago, ashe karen ya bi shi; To sai ga wannan dan acaban ya taka karen ya ji ciwo a kafarsa.”

Abin da ya faru

Ya ce da ya ga “dan acaban bai tsaya ba shi ne na bishi ina masa magana a kan me ya sa zai taka min kare kuma ba zai tsaya ya duba shi ba, ai shi ma rai ne da shi.

“Shi ne na bi dan acaban, a nan ne fasinjan da ya dauko – wani Bafulatani – ya dauki sandarsa ya kai min duka har sau biyu ina kaucewa, ya dauka nazo na rama wa karena ne.

“Ganin haka ni kuma na ciro wuka na kai masa ‘caku’ ya kauce, sai na samu dan acaban a baya, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa” inji Shetti.

Na shiga damuwa – Shetti

Ya ce ganin hakan ta faru sai hankalinsa ya tashi ya rasa yadda zai yi domin shi ba da niyyar kashe dan acabar ya bi shi ba, amma tsautsayi ya sa shi zai yi ajalinsa.

Na yi da-na-sani

Matashin ya ce ya yi da-na-sani domin shi ko cacar baki ba ta hada shi da wani, amma sai ga shi yanzu ya yi sanadiyar mutuwar mutum wanda hakan tasa aka kona gidansu.

Ya ce yana kira ga ’yan uwansa matasa da su guji biye wa zuciya, don za ta kai su halaka.