An kashe wata dalibar kwaleji da aka sassara da adda bayan an yi mata fyade a cikin coci.
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Oyo ta ce Grace Oshiagwu ta rasu ne bayan matsfan sun yi mata fyade sun kuma sassare ta.
Aminiya ta ruwaito cewa aika-aikan na zuwa ne kimanin makonni biyu da aka yi wa wata budurwa mai suna Barakat Bello fyade aka aka kuma kashe ta a yankin.
A karamar Hukumar ta Akinyele ce kuma aka yi wa wata mata mai juna biyu da ke karatu a jami’a fyade aka kuma kashe ta.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Oyo Olugbenga Fadeyi, ya kara da cewa, “Mun fara gudanar da bincike da kokarin gano miyagun domin a hukunta su.
“Muna rokon duk mai wani kwakkaran bayani da ya taimaka domin mu magance wannan danyen aiki”, inji shi