Barista Solomon Dalung daya daga cikin dattawan Arewa kuma mai fafutikar wayar da kan al’umma kan zaman lafiya, ya fito neman takarar Gwamnan Jihar Filato a karkashin Jam’iyyar APC. Ya shaida wa wakilinmu abin da ya sa ya fito takara da kudirorinsa ga al’ummar jihar:
Aminiya: Me ya karfafa maka gwiwar fitowa neman takarar Gwamnan Jihar Filato?
Solomon Dalung: Ni ban dauki wannan takara a matsayin wata bukata ko damuwa ba. Babban abin da na sanya a gaba shi ne ci gaba da gwagwarmaya da wayar wa jama’a kai kan muhimmancin zaman lafiya. Domin sai da zaman lafiya ne za a iya yin komai na rayuwa. To, ina cikin wannan hali ne sai na sami kaina a cikin wani gagarumin matsi na mutane kan na fito wannan takara. Wanda ya fi daga min hankali a cikin mutanen suka nemi na fito wannan takara, shi ne wani Bafulatani da ya taso daga wani kauye ya zo ya same ni, ya ce in na yarda na amsa fitowa takarar kujerar Gwamnan Jihar Filato. Saboda irin bayanan da nake yi kullum a kan adalci a kasar nan. Ya ce idan ban fito na yi takarar Gwamna ba, wane ne zai fito Gwamnan Jihar Filato a samu adalcin da nake ta fada. Sai na ce masa zan yi tunani, bayan da na zo na yi tunani, sai na ce idan ban fito na bayar da gudunmawata ba, wajen warware matsalolin da suke damun kasar nan, ban kyauta ba. Don haka na fito wannan takara ta kujerar Gwamnan Jihar Filato.
Aminiya: To, ganin sunan da wannan jiha ta yi kan rashin zaman lafiya, idan Allah Ya sa ka samu nasara wadanne hanyoyi za ka bi ka sake hada kan al’ummar jihar?
Solomon Dalung: Shi zaman lafiya ba wani abu ne mai wuya ba. Babban abin da zai tabbatar da zaman lafiya a kowace kasa shi ne adalci, a gudanar da harkokin gwamnati a cikin aminci, a hukunta duk wanda ya karya doka. Idan aka yi haka za a magance matsalar tabarbarewar tsaro da rashin zaman lafiya da ake fama da su a Jihar Filato. Don haka idan aka zabe ni Gwamnan Jihar, farkon abin da zan fara yi shi ne zan yi zama da al’ummar jihar, domin in nuna wa mutanen Filato alkiblata. Ni mutum ne mai ra’ayi kuma duk abin da na yarda da shi, ba ka isa ka kawar da ni a kansa ba. Zan nuna wa al’ummar Filato cewa babu wanda ya isa ya kashe wani na kyale shi, ko wane ne za a hukunta shi. Gwamnatina za ta dauki nauyi ta kare rayukan dukkan al’ummar Filato, domin hakkin ne a kan gwamanti ta kare rayukan al’ummarta, ba hakkinsu ne su kare rayukansu da kansu ba.
A lokacin da na yi Shugaban karamar Hukumar Langtang, har na gama babu wanda ya rasa ransa saboda wani tashin hankali. Don haka ba zan kyale kowa ba, ba sani ba sabo, ko kai ne coci kan Kiristanci ko kai ne masallaci kan Musulunci idan ka karya dokar kasa, zan hukunta ka idan na zama Gwamnan Filato. Idan aka fara daure masu karya doka kamar barayi masu satar kudin jama’a wallahi za a samu zaman lafiya. Abin da ya sa rikice-rikicen Jihar Filato suka ki karewa, ana daure wa mutane gindi ne ana daure wa barayi gindi ne. Saboda haka suke cin karensu ba babbaka. Amma ni Solomon ina rantsuwa da sunan Allah duk wanda ya karya doka, ko dana ne ko matata ce duk wanda ya karya doka zan hukunta shi.
Aminiya: Ganin jihar nan ta koma baya a bangaren harkokin kasuwanci da sauran al’amuran tattalin arziki, wadanne hanyoyi za ka bi ka warware wadannan matsaloli?
Solomon Dalung: Ba za a samu wani ci gaba ba a kowace kasa sai da zaman lafiya, duk kasar da ka ga ta ci gaba to akwai zaman lafiya. A yanzu idan ka je Amurka babu irin kabilar da ba za ka gani ba, za ka ga bakake ga Turawa ga Indiyawa ga Larabawa ga mutanen Natal, za ka kowane irin mutum na duniya a Amurka, kowa yana harkarsa ana zaune lafiya. Don haka idan babu zaman lafiya ba za a samu ci gaba ba. Saboda haka kamar yadda na fada babban abin da zan sanya a gaba idan na zama Gwamnan Filato shi ne samar da zaman lafiya. Ta haka ne arziki zai bunkasa ’yan jihar nan za su fita su nemi arziki ita kuma gwamnati za ta ci gaba da samun kudaden shiga ta yadda za ta bayar da ruwan sha da gyara asibitoci, a mayar da hankali kan ilimi, domin mu mutanen Filato mun gaji ilimi a Najeriya. Saboda mutum na farko da Turawa suka bai wa aikin koyar da harshen Ingilishi a Nijeriya mutumin Jihar Filato ne.
Aminiya: Kana ganin in ka samu nasara gwamnatinka za ta bambanta da gwamnatin da ke kan mulki a yanzu?
Solomon Dalung: Gwamnatinmu za ta bambanta da gwamnati mai ci yanzu a Jihar Filato, domin za mu yaf ewa kowa. Za mu ja labule kan mummunan tarihin da aka aikata a jihar nan. Kuma za mu yi zama a matsayinmu na al’ummar Jihar Filato mu yafe wa juna kan irin kura-kuran da suka faru kowa ya yi hakuri. Bayan haka sai mu kama hannu mu dauki alkawarin gina kasa, wadda ’ya’yanmu da jikokinmu za su yi alfahari da ita. Haka za mu dubi matsalolin wadanda aka lalata wa dukiyarsu mu tallafa musu. Haka su ma ma’aikatan gwamnati da aka kora ba bisa ka’ida ba, za mu duba wannan matsala.
Aminiya: Ganin irin yadda al’ummar Jihar Filato suka rungumi Jam’iyyar PDP kuma ga shi kai ka fito wannan takara a Jam’iyyar APC, ba ka tunanin za ka samu matsala?
Solomon Dalung: Mutanen Jihar Filato suna zaben mutum ne ba jam’iyya ba. Abin da ake nema a Jihar Filato a halin yanzu shi ne shugabanci nagari.
Aminiya: A karshe mene sakonka ga al’ummar jihar?
Solomon Dalung: Sakona ga al’ummar Jihar Filato shi ne ya kamata mu sani cewa a halin yanzu jihar nan tana bukatar shugaba wanda zai hada kan al’ummar jihar ya kuma kawo zaman lafiya. Don haka mu fito kwanmu da kwakwatarmu mu zabi irin wannan shugaba da zai hada kanmu a zabe mai zuwa.