Rahotanni sun ce mutumin da ya kashe mutum 49 a gidan rawar da ’yan luwadi ke sheke ayarsu, Omar Mateen ya dade yana kai ziyara gidan.
Gidan rediyon BBC ya ruwaito cewa jaridun kasar sun ambato wadansu da ke mu’amala da gidan rawar na Pulse da ke Orlando suna cewa sau dama suna ganinsa a wajen yana shan wani abu, wasu lokuta kusan sau 12.
Rahotannin suna fitowa ne bayan Hukumar Binciken Laifuffuka ta Amurka (FBI), ta ce Mateen ya yi mata waya kafin kai harin, inda ya yi mubaya’a ga kungiyar ISIS.
Sai dai Shugaba Barack Obama ya ce babu wata hujja da suka samu da ta nuna cewa an cusa wa Mateen tsattsauran ra’ayi ne daga kasashen waje.
Obama ya ce Omar ya kai harin ne sakamakon tsaurin ra’ayin addinin da ya samu a cikin Amurka.
dan takarar neman shugabancin Amurka a Jam’iyyar Republican, Donald Trump ya bayyana tsarin shige da ficen Amurka a matsayin mai rauni tunda har aka bar iyalan Omar Mateen suka shiga kasar daga Afghanistan.
Sai dai Hillary Clinton, wadda za ta yi wa Jam’iyyar Democrats takarar shugabancin kasar, ta ce za ta kawo sauye-sauyen da za su hana mallakar bindiga.
Shugaba Obama ya yi kakkausar suka ga Donald Trump, sakamakon furucinsa game da harbe-harben na Orlando.
A wani jawabi da ya gabatar a fadar White House, Mista Obama ya ce zancen da Trump ke yi na haramta wa Musulmi shiga Amurka babu abin da zai yi face yayata farfagandar masu tsaurin ra’ayi, tare da jefa Amurka cikin hadari.
Shugaba Obama ya ce, mafi abin kunya a tarihin Amurka, shi ne lokacin da ta gallaza wa ’yan kasarta saboda tsoro.
Sai dai Mista Trump, a nasa martanin, ya ce ba shi ya kashe zomon ba, rataya aka ba shi, don haka bai dace Shugaba Obama ya fusata ba.
Ya ce “Yau din nan na kalli Shugaba Obama yana cike da haushina fiye da wanda ya yi harbin nan, kuma haka mutane da dama suka ce. Haushin maharbin ya kamata ya ji ba nawa ba!”
Tuni dai Hukumar FBI ta fara yin tambayoyi ga matar dan bindigar nan, Omar Mateen, wato Noor, inda take zargin watakila ta san lokacin da ya shirya kai harin, don haka akwai yiwuwar a tuhume ta da laifin kin fallasa shi.
Gidan talabijin na NBC ya ba da labarin cewa, tunda farko matar ta yi kokarin hana mijinta kai harin.
Mateen ya dade yana zuwa gidan ’yan luwadi
Rahotanni sun ce mutumin da ya kashe mutum 49 a gidan rawar da ’yan luwadi ke sheke ayarsu, Omar Mateen ya dade yana kai ziyara…