✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matawallen Ibadan ya yaba ganawar Abdulsalam da shugabannin PDP

Matawallen Ibadan Alhaji Aminu Harande ya jinjina wa ganawar da aka yi a karshen makon jiya a tsakanin Shugaban Kwamitin Wanzar da Zaman Lafiya na…

Matawallen Ibadan Alhaji Aminu Harande ya jinjina wa ganawar da aka yi a karshen makon jiya a tsakanin Shugaban Kwamitin Wanzar da Zaman Lafiya na Kasa, Janar Abdulsalam Abubakar da shugabannin Jam’iyyar PDP inda suka mika masa korafinsu a kan zaben da ya gabata wanda tuni Shugaban Kwamitin ya mika bukatun ga Shugaba Muhammadu Buhari.

Aminu Harande ya yi wannan jinjinawa ce a zantawarsa da Aminiya a Ibadan inda ya ce, “Bayanin da muka samu cewa, dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar da Shugaban PDP na Kasa Yarima Uche Secondus da Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki da Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara sun jagoranci kusoshin PDP a ganawa da Janar Abdulsalam a Abuja alama ce, ta dorewar dimukoradiyya da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.”

Ya ce, “Mutane da yawa ba su yi zaton shugabannin na PDP za su yi irin wannan ganawa da Kwamitin na Janar Abdulsalam Abubakar ba saboda kayen da jam’iyyarsu ta sha a zaben Shugaban Kasar, inda wadansu suka fara tunanin rashin amincewarsu ga sakamakon zaben zai iya haifar da hargitsi amma sai ga shi shugabannin PDP sun fara daukar matakin kwantar da hankalin jama’a ta wannan ganawa da kuma zuwa kotu domin mika korafinsu a inda suka tabbatar za a yi musu adalci.”

Sai dai Aminu Harande wanda mai sharhi ne kan harkokin siyasar Najeriya ya nemi tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya yi koyi da tsohon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan wanda ya buga wa Shugaba Buhari waya ya taya shi murna tun kafin hukumar zabe ta kammala bayyana sakamakon zaben shekarar 2015. Ya ce, yin haka zai kara wa Atiku farin jini da karbuwa ga miliyoyin ’yan Najeriya.

Game da Jihar Oyo, Matawallen Ibadan ya ce, “A gaskiya tun farko rashin amincewar mutane da irin halayen Gwamna Abiola Ajimobi ne ya janyo faduwar APC a zaben Shugaban Kasa da ya gabata. Idan ka lura da sakamakon zaben za ka ga cewa PDP ta yi nasara a zaben Shugaban Kasa amma APC ce ta lashe mafi yawan kujerun Majalisar Dokoki ta Kasa, inda Gwamna Ajimobi ya sha kaye a zaben Sanata bayan wa’adinsa ya kare. Aukuwar haka ina ganin idan ba a yi taka-tsantsan ba yana iya haifar da gabar siyasa da ’yan Najeriya suka kyamace ta.”