Gwamnan Jihar Zamfara, ya yi zargin cewa mai gadin makarantar sakandaren GGSS Jangebe na da hannu a sace dalibai 279 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a makarantar.
Matawalle ya ce daliban sun bayyana hakan ne yayin karin bayani kan maganar da ya yi cewa sai kan mutane ya daure idan aka bayyana musu masu hannu a sace daliban.
- Batanci: JNI ta kaurace wa mukabala da Abduljabbar
- Zamfara: Zan yi murabus idan za a samu zaman lafiya —Matawalle
- An sa dokar hana fita a Jangebe
- Abin da mahaifina ya fada min a hannun ’yan bindiga —Dalibar da aka sako
“Hatta mai gadin makarantar, daliban sun ce yana ciki; sun ce bayan da masu garkuwar suka sake su, sai da suka ce musu su gaishe shi, har suka ambaci sunansa.
“Cewa shi ya ce musu su zo, kuma a gaban Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara suka fada,” inji shi.
Ya ce yaran sun ce ’yan bindigar sun cewa musu ba su san akwai makarantar ’yan mata a Jangebe be, sai da ya gaya musu ya kuma gayyace su.
Sai dai ya ce daga baya da jami’an tsaro suka je su tsare shi sai wasu bata-garin ’yan siyasa suka tayar da rikici.
“Saboda haka ana ci gaba da gudanar da bincike kuma ina tabbatar wa mutane cewa za su san duk masu hannu a cikin,” inji gwamnan.