✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matattun ma’aikata 333 ne ake karbar albashi da sunansu a Jihar Neja

A daidai lokacin da ake ci gaba da tantance ma’aikatan gwamnati a jihar Neja, wani bincike ya bankado cewa akwai kimanin tsoffin ma’aikata 333 da…

A daidai lokacin da ake ci gaba da tantance ma’aikatan gwamnati a jihar Neja, wani bincike ya bankado cewa akwai kimanin tsoffin ma’aikata 333 da su ka rasu amma ake karbar albashi da sunansu.

Hakan na zuwa ne bayan da jihar ta gano kusan Naira 207 na zirarewa daga lalitarta duk wata wajen biyan irin wadannan mutane, adadin da ya kai sama da Naira biliyan biyar a cikin shekaru biyu.

Shugaban kwamitin binciken wanda kuma shine kwamishinan ayyuka na jihar, Injiniya Ibrahim Mohammed Panti wanda ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ya kuma ce har yanzu aikin bai tsaya ba.

A cewarsa, akwai yuwuwar su kara bankado wasu ma banda wadannan.

Ya ce yawancin wadanda lamarin ya shafa akantoci ne, sai kuma wasu da dama da su ka fito daga ma’aikatar lafiya ta jihar wadanda ya ce yawancinsu su na cikin ma’aikata 80 din da aka kora a watan jiya.

Ya ce, “Daga cikin ma’aikata 27,000 da mu ke biya albashi, guda 15,907 ne kawai mu ka kai ga tantance sahihancin zamansu ma’aikata ya zuwa yanzu.

“Kazalika, akwai wasu kimanin 3,923 daga ma’aikatu daban-daban da ke da ‘yan matsaloli nan da can, wasu ma an dauke su aiki da takardun da ake zargin na bogi ne.

“Dole ne mu takawa wannan barnanr birki,” inji Panti.

Kwamishinan ya ce akwai kuma wasu ma’aikata 1,029 da sunansu ya ke a cikin rijista amma ba su halacci tattaunawar ba, wanda ya ce da zarar an kammalata za su ayyana su a matsayin wadanda babu su a zahiri.

Ya yi alkawarin cewa baya ga sallamar wadanda aka gano suna da hannu a badakalar, tilas a kuma hukunta su saboda girman tabargazar da su ka yi.