✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yau za a fara lodin fetur daga Matatar Fatakwal —NNPC

A safiyar Talata Matatar Man Fetur ta Fatakwal ta fara aiki inda ake sa ran fara sayar da man ga ’yan kasuwa

Kamfanin Man Fetur na Kasar (NNPCL) ya sanar cewa Matatar Mai ta Fatakwal ta fara aiki.

Matatar Fatakwal ta fara tace ɗanyen man ne bayan NNPC ya yi ta ɗage lokacin da za ta fara aiki bayan aikin gyaranta da aka ƙaddamar sama da shekara guda da ta gabata.

NNPC ya sanar cewa, Matatar Fatakwal ta fara aiki ne a safiyar Talata, inda ake sa ran fara jigilar man.

Kakakin NNPC, Femi Sonenye, ya ce a ranar Talata za a fara sayar man fetur ɗin matatar, yana mai cewa kamfanin na aiki tuƙuru domin ganin Matatar Warri ta fara aiki.

Lokacin da Heineken Lokpobiri ya zama Karamin Ministan Man Fetur a watan Agustan 2023, ya ce matatar mai ta Fatakwal za ta fara aiki a watan Satumba, amma sai aka jinkirta zuwa Disamba.

A cikin watan Maris 2024, shugaban NNPC, Mele Kyari, ya ba da sanarwar za a fara aikin matatar watan Afrilu.

Kyari ya jaddada kammala aikin gyaran matatar man da sauran ayyukan don bunkasa aikin tace man Najeriya, yana mai fatan Najeriya za ta zama ƙasa mai fitar da man fetur zuwa shekarar 2024.

Shekaru uku da suka gabata, gwamnati ta amince da dala biliyan 1.5 don gyara matatar, wadda aka rufe tun shekarar 2019.

Duk da kasancewar Najeriya babbar mai haƙo ɗanyen mai, Najeriya ta dogara ne kan shigo da tataccen man fetur daga ƙasashen waje saboda rashin isasshen ƙarfin tace man a cikin gida.

A watan Satumbar 2024, matatar Dangote ta fara samar da man fetur, dizal, da man jiragen sama.

Ana sa ran wannan matakin zai taimaka wajen rage tasirin cire tallafin man fetur, wanda ya ƙara farashin mai daga kusan N200 zuwa sama da N1,000 kan kowace lita.