Matatar mai ta Dangote, wadda ita ce mafi girma a Afirka, ta fara tace ganga miliyan daya na danyen mai samfurin Agbami.
Ganga miliyan dadanyen man da aka zuba a ma’ajiyar Matatar Man Dangote a ranar Juma’a da wanda kamfin ya samu za su taimaka kamfanin ya dare wajen samar da tattacen mai ganga dubu 350 a kullum.
Shugaban Rukunin Kamfanin Dangote, Aliko Dangote ya sanar cewa, “wannan babbar nasara ce ga kasarmu da ke nuna za mu iya aiwatar da manyan ayyuka cikin nasara.
“Abin da muke son cim-ma a ’yan watanni masu zuwa shi ne ganin matatar man tana aiki 100% yadda aka tsara.
- Kasuwar WAPA: Yadda uwar kasuwar canji a Nijeriya ta samo asali
- Harin Maulidi: Yadda muka tsallake rijiya da baya –Mutanen Tudun Biri
“Ina kuma burin ganin lokacin da za mu fara fitar da rukunin farko na man da muka tace zuwa kasuwannin Najeriya.”
Shugaban kamfanin Shell, wanda ya samar da danyen mai ganga miliyan daya ga Matatar Man Dangote, Osagie Okunbor, “muna maraba da fara aikin matatar man Dangote wadda za ta samar da fetur da dangoginsa ga Najeriya da suran kasashen Afirka ta Yamma.”
Ana sa ran Matatar man Dangote Dangote za ta wadata Najeriya da tataccen mai a cikin gida.
Aminiya ta gano cewa kamfanin mai na kasa (NNPCL) zai ba wa Matatar Dangote jiragen Ruwan danyen mai hudu da suka rage masa a 2023, nan da karshen shekarar.
ExxonMobil kuma zai shigo da jiragen ruwa shida da suka rage wa Matar Man Dangote.
Hakan zai ba da damar ci gaba da aikin matatar har ta fara samar da man dizel, man jirgin sama, gas din girki sannan man fetur.
Samuwar hakan, ana sa ran zai kawar da matsalar karancin man da ake fama da ita a Najeria da sauran kasashen yammacin Afirka.
Najeriya mai arzikin danyen mai ta kashe Dala biliyan 11.3 wajens shigo da tataccensa daga kasar waje a shekarar 2021.
An kuma kiyasta cewar kasar ta kashe Dala biliyan 23.3 a kan hakan a shekara 2022.