Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya ce matatar mansa da aka kaddamar za ta samar da dimbin gurabun aikin yi ga matasan Najeriya.
Ya bayyana hakan ne a Legas a lokacin kaddamar da matatar man tasa mai karfin tace danyen mai ganga 650,000 a ranar Litinin.
- Buhari da Shugabannin kasashen Afirka 5 na halartar kaddamar da matatar man Dangote
- An yi wa tsohuwa mai shekara 80 fyade a Ondo
Ana sa ran matatar, wadda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar, za ta rika samar da fitar da man fetur, dizel, man jirgin sama da kalanzir sauran dangoginsu da ake samarwa daga danyen mai.
“Aikin matatar zai samar da guraben ayyukan yi masu yawa, sannan za ta samar wa masana’antunmu muhimman albarkatun kasa da yawa,” in ji Dangote.
Shararren dan kasuwar ya kuma nuna godiyarsa kan “gagarumin goyon bayan” da ‘yan Najeriya da kuma gwamnati suka ba shi wajen samar da matatar man ta Dangote.
Ya kuma yaba wa Shugaba Buhari da ‘yan Najeriya bisa ga irin tallafin da kamfaninsa ya samu tun farkon fara aikin har zuwa kammala shi.
“Ina bayyata godiyata da na Rukunin Dangote ga ‘yan Najeriya bisa taimakon da muka samu daga shugaban kasa, gwamnatin tarayyar Najeriya, har ma da zababben shugaban kasa, domin shi ma ya taimaka.
“Haka zalika ina mika godiyata ta musamman ga Gwamna Fashola da Gwamna Ambode da Gwamna Sanwo-Olu; domin sun ba mu dukkan taimakon da muke nema.
“Muna godiya ga dukkan ‘yan Najeriya da suka ba mu goyon bayansu wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen kammaluwar aikin nan,” in ji shi.