✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashiya za ta yi sharar kotu na wata daya saboda satar tufafi

Matashiyar ta shiga shagon wata mata ta kwashi tufafi.

Wata kotun Majistiri a Kaduna, ta umarci wata matashiya ta share harabar kotun na tsawon wata 1 a matsayin hukuncin satar da ta yi na atamfa guda 6 da dogon wando 10 da kuma sket 5, wanda a kiyasce kudin kayan ya kai N82,000.

Matar da lamarin ya shafa mai suna mai suna Naomi James ‘yar shekara 25, ta amsa aikata laifin da aka tuhume ta, kana ta roki kotun ta sassauta mata.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Ibrahim Emmanuel, bai bai wa Naomi zabin biyan tara ba, sannan ya gargade ta a kan ta guji aikata laifuka.

Haka nan, Alkalin ya umarci ‘yan sanda da su maida kayan da aka kwato daga hannun Naomi ga masu shi.

Sa’ilin da yake yi wa kotun bayani, lauyan mai tuhuma, Insifeta Chidi Leo ya shaida wa kotun cewa mai karar, Ms Sarah Micheal, ta kai batun ofishin ‘yan sanda na Gabasawa a ranar 15 ga Yuni.

Sarah ta yi zargin cewa Naomi ta shiga shagonta da ke Kawo ta kwashi zannuwa shida, sket biyar da kuma dogon wando guda goma.

Bayan da ‘yan sanda suka matsa da bincike ne mai laifin ta amsa cewa lallai ta kwashi kayan.

Lauyan ya ce, hukuncin laifin da ta aikata yana karkashin Sashe na 348 da 271 na ‘Penal Code’ na Jihar Kaduna, na 2017.

(NAN)