✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matashin da ya yi kisa kan butar shayi zai bakunci hauni

Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wani matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samun sa da kisan abokinsa a kan butar shayi

Babbar Kotun Jihar Kano ta 13 da ke Miller Road, a birnin Kano ta yanke wa wani matashi hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa samun sa da kisan abokinsa a kan butar shayi.

Gwamnatin Jihar Kano ce ta gurfanar da matashin a gaban kotun a shekarar 2020, inda ake zargin sa da kisan abokinsa, Umar Garba Aisami, sakamakon rashin fahimta da ta shiga tsakaninsu a kan butar shayi.

Kotun a karkashin jagorancin Mai Ahari’a Nasiru Saminu ta ce, ta yanke hukuncin ne bisa samun hujjoji gamsassu tare da yin la’akari da Sashe na 221 na Kundin Shari’a na Final Kod na Jihar Kano.