Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta cafke wani matashi mai kimanin shekaru 18 bisa zargin sa da kashe abokinsa.
Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da mutuwar matashin mai Suna Ibrahim Khalil da ke unguwar Kofar Mazugal a Karamar Hukumar Dala ta jihar.
- Rasha ta sace Daraktan Masana’antar nukiliyar Ukraine
- An kama mutum 3 da suka yi yunkurin sace ubangidansu
Kiyawa yace, lamarin ya faru ne sakamakon sa-in-sa da aka samu tsakanin marigayin da wani mai kimanin shekaru 18.
Wanda ake zargin ne ya hasala, har ta kai ga ya hau dukan Ibrahim har lahira.
Bayan an kai shi asibitin Murtala da ke Kano, likitoci suka tabbatar da ya rasu.
Tuni dai rundunar ta samu nasarar damke matashi da ake zargin, domin gurfanar da shi a gaban kuliya.