Jami’an ’yan sanda masu binciken sirri a Jihar Yobe sun sami nasarar cafke wani matashi mai shekaru 35 a duniya da ake zargi da cin zarafin wata yarinya mai kimanin shekara uku.
Dubun matashin, wanda dan asalin garin Gusau ne a Jihar Zamfara ta cike ne a Karamar Hukumar Tarmuwa da ke Jihar ta Yobe.
- Hushpuppi: An dakatar da DCP Abba Kyari daga aikin dan sanda
- Masu yi wa kasa hidima 25 sun kamu da COVID-15 a Gombe
Ana zargin matashin ne da laifin cin zarafin karamar yarinyar mai kimanin shekara uku da haihuwa wacce ba a bayyana sunan ta ba a garin Babban-Gida da ke Karamar Hukumar Tarmuwa ta Jihar.
Kakakin ’yan sandan na Jihar Yobe, ASP Abdulkarim Dungus ne ya tabbatar da kamun a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Lahadi.
A cewarsa, tuni jami’ansu suka tsare wanda ake zargin a hannunsu, yayin da ita kuma yarinyar aka garzaya da ita asibiti don yi mata jinya da sauran gwaje-gwajen da za su zama shaidu.
Daga nan sai ASP Dungus ya ce suna kan ci gaba da gudanar da bincike don gano da ko wanda ake zargin ya aikata laifin.