Wata Kotun Majistare da ke zamanta a garin Ado-Ekiti a Jihar Ekiti, ta yanke wa wani matashi mai shekara 22, Dele Awolusi, hukuncin daurin wata daya a gidan yari bisa samunsa da laifin satar wayar salula.
Alkaliyar kotun, Titilayo Ola-Olorun, ta yanke wa Awolusi hukuncin ne bayan amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, ko kuma ya biya tarar Naira dubu 10,000.
- Badakala: Kotun daukaka kara ta rage daurin da aka yi wa Faisal Maina
- Kano ta Tsakiya: Laila Buhari ce ’yar takarar PDP —Kotu
Dan sanda mai gabatar da kara, Johnson Okunade, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar, ya aikata laifin ne a ranar 22 ga watan Nuwamba da misalin karfe 10:00 na safe a Unguwar Orere Owu da ke Ado-Ekiti.
Okunade, ya ce wanda aka yanke wa laifin ya je wurin da mutane ke cajin wayoyinsu, ya shiga wurin ya zare daya daga cikin wayoyin, kirar Infinix Smart wadda kudinta ya kai N35,000 mallakin wani mutum mai suna Ayodele Akinyemi.
A cewarsa, wanda ake tuhumar ya saba aikata laifuka, wanda ko a mako biyu da suka gabata an kama shi kan laifin satar wata jaka amma an sake shi.
Ya kara da cewa wanda ake tuhumar ya amsa laifinsa bayan samun wayar a hannunsa.
Okunade, ya ce laifin ya ci karo da sashe na 302 na Kundin Laifuka na Jihar Ekiti na 2021.