Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Osogbo, Jihar Osun, ta yanke wa wani matashi mai suna Oluwasegunfunmi, hukuncin wanke ban-daki na tsawon wata takwas bayan da ta kama shi da laifin damfara a intanet.
Kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a Ayo-Emmanuel zai yi wannan aikin ne a Makarantar Ataoja da ke Osogbo a matsayin hidima ga al’umma kamar yadda kotun ta bukata.
- ‘Har yanzu akwai ragowar ’yan matan Chibok 20 a dajin Sambisa’
- Zan bar Najeriya fiye da yadda na same ta – Buhari
Matasa su sama da biyar ne suka fuskanci hukuncin yi wa al’umma hidima a Babbar Kotun Tarayya da ke Oyo da takwararta ta Jihar Osun, bayan da aka same su laifukan zamba da damfarar mutane a intanet.
Cikin sanarwar da ta fitar a ranar Talata ta hannun shugaban sashenta na yada labarai, Wilson Uwujaren, Hukumar Yaki da Cin-hanci ta Kasa (EFCC) ta ce, ofishinta na shiyyar Ibadan ne ya gurfanar da matashin a kotun.
EFCC ta ce an kama duka matasan ne bisa laifin damfara ta intanet, tare da cewa baki dayansu sun amsa lafin da aka tuhume su da shi.
Wadanda lamarin ya shafa sun hada da Amusa Oluwasegunfunmi da Ajisafe Olaide da Lawal Morenikeji da Osuolale Abiodun da kuma Olamilekan Taofeek.
Duba da rokon sassauci da masu laifin suka yi wa kotu, hakan ya sa lauyan EFCC ya bukaci kotunan su yanke musu hukuncin da ya dace.
Hakan ya sa Alkali Iyabo Yerima ta Babbar Kotun Oyo ta yanke wa Olaide hukuncin yi wa al’umma hidima na tsawon wata shida bisa laifin samun kudi ta haramtacciyar hanya wanda hakan ya saba wa dokokin jihar.
Kazalika, su ma Morenikeji da Abiodun da kuma Taofeek, kotu ta yanke musu hukuncin yi wa al’umma hidima tsakanin mako daya zuwa wata shida, da sauransu.