✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya yi wa maraya ɗan shekara 10 kisan gilla a Zariya

Ana zargin matashin ya kashe ƙanin nasa ne saboda yaron ya ki yarda ya yi lalata da shi.

Ana zargin wani ɗan shekaru 18 da kashe wani maraya ɗan shekara 10 a yankin Ƙaramar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna.

’Yan sanda sun kama matashin ne kan zargin sa da yi wa ɗan yaron, wanda ɗan baffansa ne, ɗaurin goro tare da azabtar da shi saboda yaron ya ƙi amincewa ya yi lalata da shi.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da ta gabata a unguwar Iyan Juma da ke Karamar Hukumar Zariya.

Mahaifiyar marigayin mai suna Asama’u Mohammed ta shaida wa Aminiya cewa, “Na dawo wajen aikatau kamar yadda na saba yi don na samo abin da zan ba su su ci tare da ’yan uwansa, sai ga yayansa ya shigo a guje ya ce ga Idris can a kwance cikin jini kuma fuskarsa a kumbure, wai sun yi faɗa da wani duk an ji mishi ciwo, nan da nan na yafa hijabi ni da ɗan uwar gidana muka tafi inda yake.”

Aminiya ta garzaya Babban Ofishin ’yan sanda da ke Ƙofar Fada cikin birnin Zariya domin ji daga bakin babban jima’i, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya shaida wa wakilinmu, cewa sun tattara bayanai yadda lamarin ya kasance kuma sun tura zuwa babban ofishinsu da ke Kaduna

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna DSP Mansur Hassan ya tabbatar wa wakilin namu da faruwar lamarin, da kama wanda da ake zargi.

Ya ƙara da cewa bayan sun kammala bincike za su tora zuwa kuto.