’Yan sanda sun kama wani matashi mai suna Nasiru Dauda mai shekara 22 bisa zarginsa da yi wa budurwarsa yankan rago saboda ya bukaci ya zubar da cikin da ya yi mata amma ta ki.
Ana zargin matashin ya gayyaci budurwar tasa mai suna Salamatu Garba Jabarna mai kimanin shekara 22 zuwa bayan garin Jahun a ranar Juma’ar da ta gabata, inda ya hallaka ta.
Majiyarmu ta ce da iyayen yarinyar suka ga ba ta dawo gida ba ne suka shiga nemanta inda aka gano gawarta a wajen gari cikin wani rukunin mainoni da aka dasa domin samar da gandun daji.
Samun gawarta ke da wuya aka sanar da jami’an tsaro da Hakimin Jahun, inda ’yan sanda suka je dajin suka dauke gawar zuwa Babban Asibitin Jahun domin zurfafa bincike.
Kamar yadda wata majiya a garin wadda ta bukaci a sakaye sunanta ta shaida wa wakilimmu ta ce an zargi Nasiru da hallaka Salamatu Garba ce saboda iyayenta sun kira shi sun yi masa kashedin cewa kada ya kara zuwa wurin ’yarsu in kuma yana son ta, to ya amince a daura musu aure.
Majiyar ta ce sakamakon haka ne Nasiru ya kira Salamatu ya ba ta umarnin ta zubar da cikin da ke jikinta, amma da ta ki shi kuma ya kai ta dajin da ya yi mata yankan rago.
Majiyar ta ce da bincike ya yi nisa ne ’yan sanda suka kama Nasiru inda suka yi masa tambayoyi a ofishinsu kuma Nasirun ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa. Majiyar ta ce ana cikin yi wa Nasiru tambayoyi ne wani gungun matasa suka yi wa caji ofis din ’yan sanda na Jahun tsinke suna neman ’yan sanda su ba su Nasiru sun yanke masa hukunci da kansu.
Majiyar ta ce ganin lamarin yana neman ya yi muni ne sai ’yan sandan suka dauke wanda ake zargin zuwa hedkwatar ’yan sandan jihar da ke Dutse, kuma sai da suka yi amfani da barkonon tsohuwa kafin su tarwatsa gungun matasan.
Da yake yin wa Aminiya bayani, Nasiru Dauda ya wanke mutanen da ake zargi da hannu a hallaka budurwarsa inda ya shaida wa wakilimmu a gaban ’yan sanda cewa shi kadai ya hallaka ta bayan sun yi doguwar muhawara da kokawa, kuma ya samu nasarar yanke mata makogaro da aska ta fadi a kasa.
Ya ce ya hallaka ta ce saboda yana gudun tonon asiri domin tana da cikin wata hudu kuma ta ki amincewa ta zubar da cikin shi ne yake ganin idan ya bari zai iya samun dan gaban Fatiha ne ya sa ya hallaka ta.
Ya ce ya fadi sunayen abokansa ne domin kawai ya bata musu suna kuma daga baya ya gane cewa kazafi ba abu ne mai kyau ba saboda haka ya bukaci su yafe masa.
Ya ce ba sabon abu ba ne da aka ga dan kwalinta a dakinsa, domin suna tare tsawon shekara takwas ita ce take yi masa girki da wanki, kuma abin da ya faru tsautsayi ne kuma ya yi nadamar abin da ya aikata.
Ya musanta zargin kokarin rataye kansa bayan faruwar lamarin, inda ya ce yana gida yana wanki ’yan sanda suka kama shi, saboda duk Jahun ba ta da abokin hulda sai shi kadai. Ya ce, shi da kansa ya je gidansu ya dauke ta ranar Juma’ar da ta gabata da misalin karfe 10 na dare ya kai ta bayan gari inda ya hallaka ta.
Da yake karin haske ka lamarin Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa, SP Audu Jinjiri ya ce an gano gawar marigayiya Salamatu Garba ce a daji kusa da garin Jahun kuma an same ta an yi mata yankan rago bayan yi mata rauni a sassan jikinta.
Ya ce budurwar mai kimanin shekara 22 ’yar Unguwar kofar Gabas ce da ke Jahun, kuma tuni aka bai wa danginta gawarta domin yi mata sutura kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Ya ce ’yan sanda za su saki wadanda ya yi wa kazafi tunda ya yi ikirari da bakinsa cewa shi kadai ne ya aikata laifin. “Kuma da zarar mun kammala bincike za mu gurfanar da Nasiru a gaban kotu domin ya fuskanci hukunci,” inji shi.