✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya yi garkuwa da mahaifinsa, ya karbi fansar N2.5m

Ana ci gaba da kokarin kamo sauran ababen zargin da suka tsere.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kwara ta cafke wani matashi bisa zargin laifin yin garkuwa da mahaifinsa har da karbar kudin fansa na Naira miliyan biyu da rabi.

Ajayi Okasanmi, kakakin rundunar, wanda ya bayyana hakan, ya ce an kama wanda ake zargin ne a yankin Unguwar Kambi da ke Ilorin, babban birnin jihar.

Ya ce jami’an sashen yaki da masu garkuwa da mutane na rundunar ‘yan sandan jihar ne suka cafke wanda ake zargin ne a yayin da aka bi sawun wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne.

Okasanmi ya bayyana cewa, ana ci gaba da kokarin kamo sauran ababen zargin da suka tsere.

“Wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da cewa ya hada baki da wasu mutane biyu don sace mahaifinsa, Bature Naigboho a yankin Igboho/Igbeti na Jihar Oyo kuma ya karbi kudin fansa na Naira miliyan 2.5,” in ji Okasanmi.

Ya kara da cewa, za a mika lamarin zuwa ga rundunar ’yan sandan Jihar Oyo wadda huruminta ce kasancewar a can ya aikata laifin.