✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya tokari mahaifiyarsa ta mutu

Wani matashi a Jihar Ebonyi mai suna Ekene Ezeogo  ya tokari mahaifiyarsa  mai suna  Misis Mary Ezeugo wanda ya yi sanadin ajalinta tsohuwar mai shekara…

Wani matashi a Jihar Ebonyi mai suna Ekene Ezeogo  ya tokari mahaifiyarsa  mai suna  Misis Mary Ezeugo wanda ya yi sanadin ajalinta tsohuwar mai shekara 60. Da haihuwa wannan lamari ya faru ne a layin  Agbaja, da ke garin Abakaliki, babban birnin  jihar.

Yadda lamarin ya faru kamar yadda Aminiya ta samu labari, Ezeogo yana fada ne da kanwarsa ita kuma mahaifiyar tasu ajali ya yi kiranta ta zo tana raba su lokacin kuma ya kawowa kanwar tokari ya naushe ta  ta fadi kasa warwas  a sume. kanen wanda ya yi kisan mai suna  Onyema Ezeogo, ya ce yayansa  tokarin  uwar ya yi a ciki ta fadi kasa. Abin da ya yi sanadin mutuwar uwar su ke nan  ko motsawa ba ta yi ba,” inda a cewarsa: “lokacin da ta zo raba su fada da yayansa shi kuma sai ya daga kafa ya shure ta ta fadi a kasa.”

Babban da ga marigayiyar, wanda likita ne a asibitin Agatha  Lawrence Ezeogo, ya ce ko da aka garzayo da ita asibiti kafin ma a yi mata maganin gaugawa ta riga ta mutu sakamakon naushin kafa da Ekene ya yi mata.

Aminiya ta tuntubi mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar  Jude Madu, inda ya ce: “Sun samu labari, kuma sun kama wanda ake zargi yana da hannun. Kuma da zarar sun gama bincike za su mika shi kotu in ya so ta yi nata aikin.”