✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matashi ya roki kotu ta hana budurwarsa aure

Wani matashi a Kano, ya roki Babbar Kotun Musulinci da ke unguwar Hotoro a Kano, ta hana budurwarsa auren wani ba shi ba, saboda kudin…

Wani matashi a Kano, ya roki Babbar Kotun Musulinci da ke unguwar Hotoro a Kano, ta hana budurwarsa auren wani ba shi ba, saboda kudin da ya kashe mata.

Matashin ya ce ya kashe wa masoyiyar tasa makudan kudade saboda tsananin kaunar da yake mata, ashe ita yaudar sa take yi.

Ya ce suna tsaka da haka, kwatsam sai ya samu labari a gari cewa za ta auri wani ba shi ba.

Freedom Radio ta rawaito cewa kotun karkashin Mai Shari’a Salisu Isa Kura ta amince da bukatar matashin, inda ta hana ta auren kowa, har sai ta kammala bincike.