✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matashi ya nutse a kududdufi yana tsaka da wanke babur

Wani matashi mai shekaru 25, Ammar Ibrahim, ya nutse a kududdufi yayin da yake wanke babur dinsa na A Daidaita Sahu a kauyen Tattarawa da…

Wani matashi mai shekaru 25, Ammar Ibrahim, ya nutse a kududdufi yayin da yake wanke babur dinsa na A Daidaita Sahu a kauyen Tattarawa da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa ta Jihar Kano.

Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta jihar, Saminu Yusuf Abdullahi ne ya bayyana hakan, inda ya ce lamarin ya faru ne ranar Talata, yayin da matasin ke wanke babur din da yake sana’a da shi.

“Yana cikin wanke babur din sai santsi ya kwashe shi ya zame cikin ruwan kududdufin.

“Lokacin da muka ceto shi a sume yake, amma daga baya ya rasu.”