An cafke wani matashi mai shekara 23 bisa zargin kashe goggonsa mai shekara 60 saboda yana zargin ta da maita.
A ranar 22 ga watan Agustan 2020 ne labarin mutuwar tsohuwar da ke zaune a yankin Ipokia a Jihar Ogun ya riski ’ya’yanta, inda suka yi mata sutura aka binne ta ba tare da sun zargi kowa ba.
- Yadda rufe gidajen wasan kwaikwayo ya rage barna a Zariya
- Batanci ga Annabi: Falana ya yi karar Gwamnatin Najeriya
Bayan binne ta ne aka gano wanda ake zargin ya shiga wajen ta kafin ta mutu, lamarin da ya sa aka yi zargin ko shi ne ya kashe ta.
Bayan al’ummar yankin suka ce za su yi tsafi a kan duk wanda ke da hannu a kisan tsohuwar sai matshin ya bayyana musu cewa shi ne ya kashe ’yar uwar mahaifin nasa.
Ya ce yana kyautata zaton ita mayya ce kuma ita ta kashe dansa, ta kuma sa matarsa ta yi barin ciki.
Ko da ’ya’yan matar suka ji haka sai suka kai kararsa ga ofishin ’yan sandan yankin Ipokia.
Nan take Baturen ’Yan Sandan yankin, SP Adebayo Hakeem ya jagoranci jami’ansa suka kame wanda ake zargin.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi y ace wanda ake zargin ya amsa laifinsa.
Wanda ake zargin ya ce ya yi amfani da karfe ne ya buga wa tsohuwar a wuya saboda zargin ta da yake da hannu a mutuwar dansa na fari da kuma barin cikin da matarsa ta yi.
“Yanzu haka Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ogun, CO Edward Awolowo Ajogun ya ba da umarnin binciken lamarin a Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun.
“Kwamishinan ya bayyana takaicinsa bisa jahilcin wasu mutane masu dora laifin matsalolinsu a kan wasu da sunan maita.
“Ya ce duk wanda aka kama da laifin daukar doka a hannu ya kuka da kansa”, inji shi.
CP Edward Awolowo ya bukaci duk wani da ke da wata damuwa da ya kai ta ga jami’an ’yan sanda domin yin bincike amma ba ya dauki doka a hannunsa ba.