’Yan sanda a Jihar Ogun sun cafke wani matashi bisa zargin kashe wani direban mota Obafunsho Ismail kan musu.
Kakakin ’yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya ce lamarin ya faru ne bayan wanda ake zargin ya bugi motar mamacin ranar 8 ga watan Disamba, 2022, da misalin karfe 8 na dare.
- Ba rashin doka ba ne matsalar Najeriya —Naja’atu
- NAJERIYA A YAU: Shin ’Yan Najeriya Sun Gamsu Da Kayyade Cire Kudi?
“Mamacin ta fito daga motarsa don duba irin barnar da matashin ya yi wa motarsa.
“Sai wanda ake zargin ya ki fitowa daga motarsa ya fara kokarin guduwa, nan take musu ya kaure a tsakaninsu.
“Bayan ya fito daga motar ba jimawa ya sake komawa ya ja ta a guje ya bi ta kan mutumin da ya yi wa barna,” in ji shi.
Kakakin ya ce daga baya jami’an rundunar sun gudanar da bincike tare da cafke matashin.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ogun, Lanre Bankole, ya bayar da umarnin mika matashin zuwa sashen binciken manyan laifuka na runduar.
Ya ce za a gurfanar da shi a gaban kotu da zarar an kammala bincike.