✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya kashe tsoho da tabarya saboda zargin maita a Gombe

Matashin yana zargin tsohon ne ya kama shi ya kwanta rashin lafiya

Rundunar Yan Sandan Jihar Gombe ta cafke wani matashi mazaunin yankin Panda a Karamar hukumar Akko ta Jihar Gombe bisa zarginsa da kashe wani tsoho ta hanyar duka da tabarya.

An kama matashin ne mai suna Salisu Lawan, mai kimanin shekara 30, sannan aka gabatar da shi ga manema a Gombe, ranar Laraba.

Da yake gabatar da wanda ake zargin a hedkwatar rundunar, Kakakinta, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya ce a ranar 4 ga watan Agusta na shekarar 2023 ne wani Mai suna Mohammad Usman Mai shekara 26 da ke zaune a garin na Panda ya kai rahoto ofishin ’yan Sanda na garin Kumo.

A cewar Kakakin, wani mai suna Salisu Lawan da suke zaune a gari na Panda ya yi amfani da Tabarya ya bige mahaifinsa, Usman Bello, mai shekara 65 bisa zargin maita, wanda hakan ya zama ajalinsa.

Ya ce sun dauki mahaifin nasu zuwa babban asibitin garin Kumo inda likita ya tabbatar musu da mutuwarsa.

Wanda ake zargin, Salisu Lawan, ya ce wata rana ce da safe, wajen misalin karfe 7:00, rashin lafiya ta kama shi ya kasa cin komai har karfe 7:30 na yamma, inda a lokacin da yake kwancen yake kiran sunan shi wanda ya kashe din, wato Mani Shugaba.

Da ake tambayarsa ko me ya sa ya dauki doka a hannunsa sai ya ce shi bai san lokacin da hakan ta faru ba domin ba ya cikin hayyacinsa, ’yan uwansa ne suka ce masa da yake kwance yana ta kiran suna Mani Shugaba, shi ne shi kuma yake zargin sa da maita a kan shi ne ya kama shi.

Salisu, ya ce yana nadamar abin da ya aikata domin bai san lokacin da ya yi hakan ba saboda ganin abin yake kamar a mafarki.

Ganin ya shiga hannun hukuma ya nemi a yi masa sassauci saboda fada masa aka yi Mani Shugaba maye ne, kuma shi ya kama shi.

Shi dai Salisun har masallacin yabi Mani Shugaba bayan ya yi sallah ya buga masa tabarya a ka, nan take kuma ya fadi a kasa.

Daga nan sai Kakakin ’Yan Sandan ya ce da zarar sun kammala bincike za su tura wanda ake zargin a gaban kotu.