Babbar kotun Legas ta kama wani matashi mai suna Sunday Hycient da laifin kisan wani abokinsa akan rikicin da ya hada su, akan naman kare.
Kotun dai ta dage karar har zuwa ranar 19 ga Fabarairu 2019, kamar yadda alkalin kotun ya sanar Mai shari’a Coker.
Kotun dai na tuhumar Sunday ne akan kashe abokinsna mai suna Onwe Ozoemelem ta hanyar naushinsa a kirji a kusa da gadar Festac Link Bridge, da ke Legas, wasu masu tukin keken Napep ne suka kai shi asibiti daga bisani kuma ya rasu.