✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matashi ya harbe kaninsa yayin gwada maganin bindiga

An yi rashin sa’a maganin bindigar bai yi aiki ba.

Wani matashi ya harbe kaninsa mai shekaru 12 yayin gwada maganin bindiga a Karamar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara.

Wadandan lamarin ya shafa dai ’ya’yan wani mafarauci ne da suka mallaki wani sabon maganin bindiga kuma suka yi yunkurin tabbatar da ingancinsa.

Lamarin a cewar wakilinmu ya faru ne a ranar Lahadi, inda wanda ya yi aika-aikar tuni ya arce ya bazama cikin jeji bayan mai aukuwar ta auku.

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Litinin, jami’in hulda da al’umma na rundunar ’yan sandan jihar, Okasanmi Ajayi, ya ce Kwamishina ’Yan sanda Paul Odama ya ba da umarnin a soma bincike a kan lamarin.

“Bayan sun daura maganin bindigar a jikinsu, sai babban cikinsu ya yi amfani da bindigar mahaifinsu ta farauta ya harbi kaninsa.

“Sai dai an yi rashin sa’a maganin bai yi aiki ba, lamarin da ya sanya nan take kanin da aka harba ya shura,” a cewar Okasanmi.

Okasanmi ya shawarci iyaye da suka rika zuba idanu kan duk wani motsi na ’ya’yansu domin gudun faruwar mummunan tsautsayi makamancin wannan.