✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matashi ya hallaka kanwar mahaifiyarsa bayan sace wayarta

Ya sace wayoyin matar bayan aikata lahira da tabarya

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta cafke wani matashi mai shekara 18 bisa zargin kashe matar aure da tabarya, sannan ya raunata ’ya’yanta biyu a kokarin sace mata waya.

An dai cafke wanda ake zargin, Abdulsamad Suleiman, tare da wani mai shekara 17 mai suna Mu’azzam Lawan.

Matar, mai suna Rukayya ta gamu da ajalinta ne ranar 12 ga watan Fabrairun 2022, a unguwar Danbare da ke Kano.

’Ya’yan marigayiyar su ma, sun hadu da gamonsu a hannun wanda ake zargin, inda ya lakada musu dukan kawo wuka da tabaryar da ya yi ajalin mahaifiyarsu.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da kuma cafke wanda ake zargin.

A cewar kakakin, a cikin wata sanarwa, wanda ake zargin ya amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar 12 ga watan Fabrairun 2022.

Kiyawa ya ce, “Bayan ya gaishe ta, ya hangi wayoyi guda uku kuma ya sace su. Ganin cewar ta gane shi, sai ya yi amfani da tabarya ya dinga dukanta a kai sannan ya doki ’ya’yanta biyu, kafin daga bisani ya tsere da wayoyin.

“Ya amsa cewar ya bai wa abokinsa kyautar daya daga cikin wayoyin, kana ya sayar da guda biyun kan kudi N12,000.

“Shi ma abokin nasa ya amsa sayar da wayar da aka ba shi kan kudi N12,000,” cewar kakakin ’yan sandan.

Ya ce za a mika wadanda ake zargin gaban kotu da zarar an kammala bincike don su girbi abin da suka shuka.