Wani matashi mai shekara 18 ya gurfana a gaban Babbar Kotun da ke zamanta a Zuba, Abuja bisa zargin wani mutum da wuka a gefen ido.
Lauya mai shigar da kara, Chinedu Agada, ya bayyana wa kotun cewar wanda yake karewa ya shigar da koke kan matashin da ya yi masa aika-aikan ne a cajis din da ke Gwarinpa a ranar 25 ga Oktoba, 2020.
- PDD ta bukaci Kotun ICC ta hukunta tsoffin Hafsoshin Tsaro
- Kotu ta daure ma’aikaci saboda satar kayan N1.5m
- Kotu ta ba mayu awa 24 su warkar da mara lafiya
Ya ce wanda ake zargin ya gayyaci abokansa su 10 a lokacin da mai karar ke hanyarsa da zuwa sayen katin waya a unguwar Kado, inda inda suka yi masa dukan kawo wuka.
Lauyan ya kara da cewa maharan sun yi wa mai karar rauni da wuka a gefen ido, gwiwa da kuma hannunsa.
Ya ce an garzaya da wanda aka yi wa raunin asibitin Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC), da ke Gwarinpa, inda ya kashe kudin magani N15,160.
Sai dai wanda ake zargin ya musanta aikata laifukan da ake tuhumarsa a kansu a gaban kotun.
Alkalin kotun, mai shari’a Gambo Garba, ya ba da belin wanda ake karar kan N100,000 sannan ya gabatar da wanda zai tsaya masa a kotu.
Daga nan ya dage zaman kotun zuwa ranar 3 ga watan Maris, 2021, don ci gaba da sauraren shari’ar.