✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya datse kan abokinsa saboda babur

Wani matashi mai suna Safas Afa, dan shekara 20 da haihuwa a Jihar Edo ya datse kan abokinsa mai suna Aniete Okon, wanda hakan ya…

Wani matashi mai suna Safas Afa, dan shekara 20 da haihuwa a Jihar Edo ya datse kan abokinsa mai suna Aniete Okon, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Matashin dai ya kashe abokinsa ne bayan da ya tabbatar ya mutu sai ya dauke babur dinsa da kuma wayar salularsa ya tafi da su ya sayar kan kudi Naira dubu 160. Yanzu haka mai laifin na tsare a hannun rundunar ’yan sandan jihar. Wannan aika-aika an yi ta ne a kauyen Okomu da ke yankin karamar Hukumar Obia ta Yamma. .

A bayanin nau’in irin laifin da Kwamishinan ’yan sandan Jihar Edo Haliru Gwandu ya yi wa manema labarai, ya ce Afa yaudarar abokin nasa ya yi da ya zo ya raka shi gona, bayan sun isa gonar ce ya makure shi, har sai da ya suma daga bisani ya sanya adda ya sare masa kai.
”Ce wa abokina na yi mu je ya raka ni gona, inda ya dauke ni a kan babur dinsa, muna tafiya daman na boye adda. Hakan kuwa aka yi,” in ji shi.
Da yake yi wa manema labarai karin bayani dangane da zargin kisan kai da ake yi masa matashin Safas Afa, ya ce shi ya kashe abokin nasa ya datse masa kai ya boye sannan ya tafi da wayar salularsa da babur dinsa ya je wani kauyen Okomu, ya sayar a can nema mutanen kauyen suka kama shi, bayan ya sayar da babur din kan Naira dubu160.