Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta yi nasarar cafke wani matashi mai shekara 30 bisa zargin sa da yin garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa.
Ana zargin matashin da yin garkuwa da wasu mutum biyu masu suna Fatsuma Buba da Manu Adamu a Karamar Hukumar Nafada a jihar.
- Ganduje na mana kafar ungulu —Kwamitin karbar mulkin NNPP
- An kashe hatsabibin dan ta’adda ya je garkuwa da dan kasuwa a Katsina
Da yake gabatar da matashin ga ’yan jarida, kakakin rundunar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya ce ’yan sanda sun samu rahoton wanda ake zargin ne ta hanyar kira a waya, daga nan suka yi hadin guiwa da maharba suka shiga daji suka ceto wadanda aka yi garkuwa da su din ba tare da an ji musu rauni ba.
Ya ce bayan kama wanda ake zargin a maboyarsu, an kwato dabbobi guda 40 da wayar salula da kuma makamai.
Ya ce wani mazaunin karamar hukumar ta Nafada ne ya kai wa ’yan sandan rahoto cewa wasu mutane dauke da bindiga da adduna sun shiga kauyensu mai suna Papa suka ji wa ’yan uwansa rauni sannan suka yi awon gaba da Fatsuma da Manu.
Daga samun rahoto rundubar ta fara binciken sirri ta kuma gano maboyar wadanda ake zargi da yin garkuwa da mutanen, aka kama kama shi aka tseratar da wadanda a aka yi garkuwa da su din.
Ya ci gaba da cewa ’yan sanda sun garzaya da wadanda aka tseratar din zuwa asibiti inda aka duba lafiyarsu.
Da Aminiya take zantawa da wanda ake zargin, ya ce shi bai san komai ba, yana wajen kiwo ne kawai ’yan sanda suka zo za su kama wansa, amma da ba su sami wan nasa ba, sai suka kama shi.
A cewarsa, bai san abun da wan nasa ya aikata ba da aka zo neman sa ya gudu.
Ya ci gaba da cewa wan nasa ya dauko shi ne yana masa kiwo.