Fasto Ayo Oritsejafor, Shugaban kungiyar Kiristoci Ta Najeriya (CAN) ne ya kirayi dukkan masu rike da madafun iko a Najeriya da su sadakar da rabin albashinsu na tsawon shekara daya ga matasan kasar nan, da nufin magance matsalar rashin aikin yi da ke addabar matasan.
Tun lokacin da Faston ya yi wannan kira, har yanzu ban ji inda ya kara yin bayani ba, na cewa ko ya samu wanda ya amsa kiran nasa, ko a’a ba. Ni kuwa da ma na san ba zai samu mutum ko daya da zai amsa kiran nasa ba, domin kuwa a Najeriya, batun na daukewa ne ba na bayarwa ba. Babban abin da muka kware shi ne, haifar da talauci ga matalauta, da hana aikin yi. Don haka, ba su gajiya da daukewa, abin da suke dauka kuma ba ya isar su, balle har su ce za su ba da wani abu daga ciki. Kaico!
Kana neman cin zabe domin hawa kujerar mulki a Najeriya? Sai ka koyi yadda za ka shirga wa mutane karya, ka koyi yadda za ka tafka cuta, sannan ka koyi yadda za ka iya tafka kasurgumar sata. Idan ka samu mulkin, abin da za ka yi ke nan, sannan kuma ka kalli tsabar idanun mutane, ka gaya masu dukkan irin kalaman da ka san suke son kunnuwansu su ji. Ba ka da kaico, domin sun riga sun gama yi maka mai wuyar, tun da dai sun zabe ka. Takaicin ya rage nasu, tun da sun maida kansu wawaye!
Abu ne da kowa ya sani cewa, a lokacin da za a tsefe ministoci, sukan hada baki da ’yan Majalisar Tarayya, domin yi wa juna alkawarin kason da kowa zai samu idan sun amince da Ministan, kamar kuma yadda suke taimakon juna wajen amincewa da kasafin kudin ma’aikatarsu. Haka su ma kwamishinoni kan yi da ’yan majalisarsu na jiha. Wasu lokuta, ministoci kan hada baki da bara-gurbin jami’an bankuna da ’yan kwangila domin aiwatar da satarsu. Wasu gwamnonin kuwa, tuni suka kware wajen sace dukiyar al’ummar jihohinsu, suna mayar da su na kashin kansu.
A wasu jihohin kalilan na Najeriya, akan samu gwamnonin da ba su kasance beraye ba. A nan za ka rika ganin ayyukan ci gaban al’umma suna gudanuwa. Inda kuwa aka samu gwamna ya zama mahandami mai hadama, za ka ga daga shi sai iyalansa, sai kuwa wadanda suka rabe shi ne kadai suke fantamawa.
Ga alama dai al’amura sun fada canzawa. dauki misalin abin da ya faru a Jihar Delta makon jiya, inda Matasan Isoko suka harzuka, a lokacin da manyan jam’iyyar PDP ke taro a Idheze, suka tarwatsa su. Sai ga manya na gudun ceton rai a kan titi, wasu ma suna tsallake shingaye, kai ka ce Iyabo Obasanjo ce ke gudun tsere wa EFCC.
Abin da matasan suka rika fadi shi nne: “Dukkansu da kuka gani ’yan 419 ne.” Wani daga cikinsu kuwa sai ya ce: “Da zarar an kammala zabe, ba ka kara ganin keyarsu. Amma da an ce maka zabe ya karato, sai ka same su sun lababo zuwa gare mu… mu kuwa mun ce ba za mu yarda ba a wannan karon. A wannan karon, za mu kare hakkinmu da iyaka karfinmu!”
Abin da nake so a lura da abin da matasan nan suka fada shi ne: ‘iyaka karfinmu.’ Mu dubi abin da ya faru a Kaduna, lokacin da aka gudanar da gangamin goyon bayan Jonathan. Lallai kam matasa sun nuna karfinsu, har ma jini sai da ya zuba. Mu hankalta dai, domin fa har yanzu lokacin zaben bai ma fa zo ba!
Shi wannnan gangami na Jonathan a Kaduna, an samu bayanin cewa wani gwamna ne daga Kudu-Maso-Kudu ya dauki nauyinsa a kan Naira miliyan 500 da nufin bunkasa martabar Jonathan a Arewa.
A inda muka fara ganin alamun abin da zai wakana na nuna karfi a nan gaba, shi ne inda wanshekare da gangamin sai ga Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Olufemi Adenike ya fito karara, kamar wani kantoman soja, yana cewa: “Daga yanzu, ba za mu lamunce wa wani mutum ko wata kungiya su sake hada gangami ba tare da amincewar hukjumar ’yan sanda ta jiha ba.”
Ni kuwa na ce, kila dai Mista Olufemi bai samu damar leka kundin tsarin mulkin Najeriya ba, kafin ya fadi haka. Domin kuwa ai shi ne ya ba ’yan kasa damar shirya taruka da gangami kuma babu wani da zai ce ya haramta masu haka. Dalili ke nan ma tun da kwamishinan ya yi wannan batu, ’yan rajin kare ’yancin ’yan Adam suka fara amayar masa da martani, cewa ba za ta sabu ba, wai bindiga a ruwa. Haramta taro ko gangami na lumana, babu mai ikon haramta su, tun da hakkin ne na ’yan kasa.
Irin yadda cin hanci da rashawa ya zama ruwan dare a Najeriya, yadda yaje-yajen aiki ke kara yawa, yadda dukiyar kasa ta koma mallakin wasu tsirarun jami’an gwamnati, lallai lokaci ne da ya kamata a yi karatun-ta-natsu. Lokaci ne da ya kamata a gaya wa Fasto Oritsejafor cewa, matasanmu ba sadaka suke nema ba, abin da suke son gani shi ne adalci daga masu mulki. Adalcin nan ne zai samar masu da abin yi, ya samar masu da abinci amma ba sadaka ba.
Matasanmu adalci suke so ba sadaka ba
Fasto Ayo Oritsejafor, Shugaban kungiyar Kiristoci Ta Najeriya (CAN) ne ya kirayi dukkan masu rike da madafun iko a Najeriya da su sadakar da rabin…