✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasan Yobe sun yi zanga-zanga kan yawaitar fyade da satar mutane a Arewa

Sun ce matsalolin Arewa na ci musu tuwo a kwarya

Wata kungiyar matasa a garin Potiskum na jihar Yobe ta gudanar da zanga-zangar lumana da tattaki kan yawaitar matsalar tsaro a Arewacin Najeriya.

Kungiyar ta ce ta dauki matakin ne don nuna fushinta da yadda ake yi wa yara mata fyade, garkuwa da mutane da kuma tabarbarewar ilimi a Arewa, a ranar Talata.

Da yake zantawa da manema labarai a sakatariyar Karamar Hukumar Potiskum, shugaban kungiyar, Kwamared Aliyu Haruna ya ce “Mun fara wannan zanga-zangar lumana ne duba da yadda ilimi ya tabarbare a Arewa da kuma matsalar tsaro da ke addabar al’umma da  yadda ake yi wa kananan yara da ’yan mata ’ya’yan talakawa marasa galibu fyade ana barin su ba su da wata madafa.”

Ya kara da cewa, “A matsayinmu na matasa, mun damu da halin da suke ciki don sanar da jama’a hakan ta hanyar zanga-zangar lumana don kyautata rayuwar ’yan uwanmu masu zuwa.

“A cewarsa, ba mu da ’yanci shi ya sa muke ta da murya a cikin al’umma don taimakawa ci gaban al’ummarmu wadda watakila ta bin wannan hanya kan iya masu ruwa da tsaki na jagorancin kasar nan kan iya daukar mataki a kai.”