Wakilin kungiyoyin matasan Katsina, Aliyu Idris Zakari, ya shelanta cewa matasan jihar ba za su shiga wannan zanga-zangar dake tafe kan tsadar rayuwa a Najeriya ba.
Aliyu Idris Zakari ya ce sun yanke shawarar kaurace wa zanga-zangar ce bisa lura da suka yi da irin abubuwan da suka faru a wasu kasashe irin suLibiya da abin da ke faruwa a Kenya a halin yanzu.
Bisa haka ne suka nesanta kansu daga shiga cikin wannan zanga-zanga duk da cewa sun san sauran takwarorinsu a kasar da za su shiga.
Su ma ’yan kasuwar jihar Katsina, sun kaurace wa zanga-zangar, saboda a cewarsu, a karshe a kansu abin ke karewa, inda ake barnata masu dukiya.
- NCC ta umarci a sake buɗe layukan mutane da aka rufe
- Zanga-zanga: Gwamnatin Katsina ta kira taron gaggawa
’Yan kasuwar sun nemi gwamnati da ta nemo sauran kungiyoyi don zama a samo hanyoyin da ya dace don samun zaman lafiya da kawo saukin rayuwa a jihar da ma kasa baki daya.