Majalisar Dattawa ta ce fiye da kwalaben maganin kodin miliyan uku mata da matasa suke sha don gusar da hankulansu a jihohin Kano da Jigawa.
Batun ya bayyana ne lokacin da Sanata Baba Kaka Bashir Garbai dan jam’iyyar APC daga jihar Barno da wasu sanatoci 37 suka goyi bayan kudurin da zai binciki karuwar ta’adar shan miyagun kwayoyi a tsakanin matasa.
Kudurin wanda Sanata Jibrin Barau dan jam’iyyar APC daga Jihar Kano ya amince da shi ya ce bincike ya nuna cewa masu shan maganin kodin don su gusar da hankulansu a jihohin Kano da Jigawa suna shan kwalba uku zuwa takwas a rana.
Ya bayyana cewa yayin da ake samun karuwar shan magungunan mura don gusar da hankali a yankin Arewa maso yamma, bincike ya nuna cewa ana samu karuwar shan muggan kwayoyi a jihar Borno da ke yankin Arewa maso gabas sakamakon rikicin boko haram.