Bincike ya gano cewar wasu matasan kabilar Irigwe ne suka kai farmaki tare da kashe wasu Fulani matafiya 25 a garin Jos, yayin da wajen 50 suka bace.
Wani daga cikin matafiyan da ya tsallake rijiya da baya a harin, Muhammad Ibrahim, ya shaida wa Aminiya cewa an kai musu harin ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta dawowa daga Jihar Bauchi inda suka je domin halartar taron bikin Sabuwar Shekara Musulunci da aka gudanar.
– ’Yan sanda sun ceto shugaban Jam’iyyar APC a Neja
– An kori dan sandan da ya kashe wani mutum daga aiki
A cewarsa, wasu ’yan daba ne suka tare motocin nasu da ke kan hanyarsu ta komawa zuwa jihohin Ondo da Ekiti.
Wakilinmu ya ziyarci Asibitin Kwararru na Filato inda ya gane wa idonsa gawar mutum 15 da aka kai asibitin; Wasu daga cikin matafiya da suka rasa ransu a harin kuma an ajiye su a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Filato, ASP Ubah Gabriel, ya shaida wa wakilin namu cewa sun Rundunar samu rahoton faruwar wani al’amari a yankin Gada-Biyu, amma an tura jami’ansu tsaro don tabbatar da abin da ke faruwa.
Kazalika, ya yi alkawarin yi mana cikakken bayani game da lamarin daga baya.
Tuni Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar ta Filato da wasu manyan jami’an tsaro a jihar suka ziyarci asibitin don gane wa idonsu yadda lamarin ya faru.