✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasan Dawaki sun kafa kwamitin gyaran tarbiya a Bauchi

kungiyar Matasan Dawaki da ke garin Bauchi ta kafa kwamitin gyaran tarbiyya.Shugaban Kwamitin matasan unguwar Dawaki Malam Zakariya Umar ne ya bayyana wa Wakilin Aminiya…

kungiyar Matasan Dawaki da ke garin Bauchi ta kafa kwamitin gyaran tarbiyya.
Shugaban Kwamitin matasan unguwar Dawaki Malam Zakariya Umar ne ya bayyana wa Wakilin Aminiya a lokacin da suka tattaunawa a Bauchi a makon jiya.
Ya ce sun kafa kwamitin ne tun lokacin da mai Martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu ya ba masu unguwanni da kungiyoyi umarnin kafa wani kwamiti wanda zai rika sa ido game da gyaran tarbiyyar matasan da suke ta’ammali da shan miyagun kwayoyi.
Ya ce a yanzu sun dukufa wajen wayar da kan matasa ta yadda za su nisanci shan miyagun kwayoyi da kuma aikata munanan aiyuka.
Ya ce “Akwai da yawa daga cikin matasan da suka tuba daga aikata sara-suka, kuma da yawa daga cikinsu sun fara koyon kananan sana’oi domin rufa wa kansu asiri. Don haka a matsayina na sabon shugaban kwamitin kungiyar zan ci gaba da shiga kafafen watsa labarai domin wayar da kan matasan Najeriya.”
Ya ce tun lokacin da suka kafa wannan kwamiti mai suna (Dawaki Youths Progrissibe Forum) duk wanda yake zaune a unguwar ya fahimci kashi 75 cikin 100 na matasan unguwar sun gyara halayensu.
Ya bukaci jama’a su rika ba kwamitin nasu goyon baya ta yadda za a ci gaba da gudanar da ayyukansa.