Rundunar tsaro ta bigilanti a jihar Kano ta ce ta samu nasarar kama wasu matasa uku da suke yawo cikin unguwanni suna satar kayayyakin al’umma bayan sun saci wata akuya.
Dubun matasan ta cika ne a kan titin gidan gona dake tsakanin unguwar Dandinshe da kuma wani bangare na Kurnar Asabe da ke Karamar Hukumar Dala a cikin birnin Kano.
- INEC ta ba Adeleke takardar shaidar lashe zaben Gwamnan Osun
- BIDIYO: Yadda Hana Tukin Adaidata Sahu Da Daddare Zai Shafi Rayuwarmu — Kanawa
Matasan, da aka bayyana sunansu da Usman da Bilal da Abba, sun fada hannun jami’an na bijilanti ne karkashin jagorancin Mataimakin Kwamandan Rundunar ta Jihar Kano, DC Danlami Akibu.
Danlami ya ce, “Matasan suna yawo a babur din Adaidata Sahu kuma suna dauke da makami wajen tsorata mutane su kuma kwace musu kaya.”
Yayin da aka yi bajekolinsu dai sun amsa dukkan laifukan da ake zarginsu da aikatawa kuma sun ce ba wannan ne karo na farko da suke wannan laifi ba.
Sai dai sun bayyana nadamarsu tare da cewa ba za su kara aikata hakan ba a nan gaba.
Mataimakin Kwamandan bijilantin ya kara da cewar da zarar sun kammala bincike za su mika wadanda ake zargin ga Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano domin ci gaba da gudanar da bincike a kansu.