Sanata mai wakiltar Bayelsa ta Gabas, Ben Murray Bruce ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya manta yadda matasan Najeriya da yake kira da malalata suka tsaya cikin rana mai tsananin zafi suka zabe shi.
“Maimakon Buhari ya bincika ya gano dalilin da ya sad a yawa daga cikin ‘yan Najeriya suke fita kasashen waje kamar su Kanada domin aiki, Shugaban Buhari sai yake kiransu da malalata.
“Abin ban dariya a nan shi ne yadda wadannan matasan suka tsaya cikin tsananin rana na tsawon lokaci domin su zaba mutumin da yi alkawarin kawo canji, amma sai ya bige da kawo sarka.”