✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasan Benuwe sun yi zanga-zangar kisan da ake yi musu

Mazauna garin Makurdi jiya sun yi jerin gwano a kan hanyoyin garin don gudanar da zanga-zanga kan kisan da wasu ’yan bindiga suka yi wa…

Mazauna garin Makurdi jiya sun yi jerin gwano a kan hanyoyin garin don gudanar da zanga-zanga kan kisan da wasu ’yan bindiga suka yi wa jama’ar kananan hukumomi biyu na jihar inda suka yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da kashe-kashen da ke faruwa a sassan jihar ko ya sauka daga kan mukaminsa.
 
Yayin da yake mayar da martani kan hare-haren, Buhari  ya bayyana su a matsayin abin da ba za a amincewa ba inda ya baiwa jama’a tabbacin kamewa tare da ladaftar da maharan.
 
Masu zanga-zangar galibi matasa, sun tare hanyoyin jihar inda suka yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta shiga cikin jihar tare da kawo karshen lamarin.