Wasu matasa a jihar Kano sun shirya ta su salon zanga-zangar lumana, inda suka fito tsabtace hanyoyi da sunan share kazantar masu zanga-zangar EndSARS a wasu titunan jihar.
A yayin share titunan da tsintsiya, matasa sun kira gwamnati da lallai ta dauki matakin gaggawa kan rashin tsaro a yankin Arewacin Najeriya, suna masu amfanin da alamomin sakonni kamar haka: #SecureNorthernNigeria #SecureNorth – Ma’ana #AceciArewacinNajeriya #ACeciArewa.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wasu matasa ke tsaka da gudanar da zanga-zangar nuna adawa da rundunar ’yan sanda ta SARS a fadin Najeriya.