✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasa sun kori jami’an kashe gobara a Kasuwar Jalingo

Akalla shaguna 30 sun kone a gobarar da ta tashi a kasuwar yankin Road Block da ke Jalingo, Jihar Taraba.

Fusatattun matsa sun kori jami’an kwana-kwana da suka je kashe gobarar da ta tashi a kasuwar yankin Road Block da ke Jalingo, babban birnin Jihar Taraba.

Matakin kida da duwatsu da matasan suka dauka ya mayar da hannun agogo baya a kokarin kashe gobarar, inda wutar ta ci gaba da barna.

Daga bisani an tura ’yan sanda sun tarwatsa matasan kafin jami’an suka samu damar shawo kan gobarar.

Akalla shaguna 30 ne dai aka tabbatar sun kone a sakamakon gobarar ta safiyar Asabar.

’Yan kasuwar da gobarar ta shafa sun ce sun yi asarar dukiya ta miliyoyin kudi.

Ba a kan ga gano musabbabin tashin gobarar ba, amma wasu ’yan kasuwar na zargin masu sayar da gas din girki da masu sana’ar wanda a kasuwar da zama sila.