✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matasa sun kone ‘matsafa’ a gaban ofishin ’Yan sanda a Ogun

Abun takaici ne ganin yadda matasan suka dauki doka a hannunsu.

Wasu fusatattun matasa sun kone wasu ma’aurata da ake zargi da tsafi bayan an kama su da sassan jikin mutum a yankin Oja-Odan da ke Karamar Hukumar Yewa ta Arewa a Jihar Ogun.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, a ranar Asabar da ta gabata ce fusatattun matasan suka fasa wani ofishin ’yan sanda a yankin inda suka fito ababen zargin biyu suka yi masu dukan kawo wuka sannan suka banka musu wuta.
Ko da yake zuwa yanzu jami’an tsaron ba su kai ga bayyana sunayen wadanda ake zargin da lamarin ya rutsa da su ba, sai dai bayanai sun nuna cewa ’yan sanda sun cafke mata da mijin ne bayan samunsu da sassan jikin mutum a cikin wani buhu a dakinsu na aure.
Lamarin wanda ya faru a yankin Oja Odan a Jihar Ogun ya sanya rundunar ’yan sandan jihar fitar da sanarwa ta musamman wadda take yi wa al’ummar jihar kashedi da su guji daukar doka a hannu.
A sanarwar da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar Ogun, DSP Abimbola Oyeyemi ya fitar ya shaida cewa abun takaici ne ganin yadda matasan suka dauki doka a hannunsu.
Ya ce da sanyin safiyar Asabar ne wasu mutane masu mutunta doka suka mika wa ’yan sanda mutanen biyu da ake zargi da samunsu da sassan jikin mutum, “jami’anmu sun tsaresu a caji ofishin ’yan sanda suna yi masu tambayoyi sai fusatattun matasa masu tarin yawa suka shigo, wanda a dalilin haka suka ci karfin ’yan sandan, inda suka fitar da wadanda ake zargi suka yi masu dukan kawo wuka, suka kashe su sannan suka kuma babbake gawarsu.”
Abimbola Oyeyemi ya ce abun takaici ne danyan aikin da masu aika-aikar suka aiwatar, domin wanda ake zargi laifi ba ya tabbata a kansa har sai an yi bincike an gabatar da shi a kotu ta tabbatar, kuma daukar doka a hannu ba ya taba hallata.