✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matasa sun kona ofishin ’yan sanda a Sakkwato

Matasa sun fusata kan lallai sai an sako musu wasu mutum biyu da ake zargi da garkuwa da mutane.

Rahotanni daga jihar Sakkwato sun tabbatar da mutuwar wani mutum daya tare da konewa wani ofishin ’yan sanda da wasu motoci biyu a Karamar Hukumar Kware ta jihar.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar ASP Abubakar Sani ya fitar, ta ce lamarin ya faru ne bayan da wasu gungun matasa suka nemi a sako musu wasu mutum biyu da ke daure a caji ofis kan zarginsu da ta’adar garkuwa da mutane.

Kamar yadda sashen Hausa na BBC ya ruwaito, an kama mutanen da ake zargi da garkuwa da mutane inda ake ci gaba da gudanar da bincike a kansu.

Sai dai a yayin da suke tsare a hannun jami’an tsaro, wasu gungun mutane wadanda galibi matasa ne suka je har caji ofis suna ihun a saki mutanen biyu kamar yadda ASP Sani ya bayar da shaida.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan ya ce ana tsakar haka ne matasan suka mamayi jami’an tsaron da ke kula da ofishin ’yan sandan suka cinna masa huta har da motar DPO da wasu motocin ’yan sanda biyu.

Ya ce, matasan sun kashe daya daga cikin mutanen da ake zargi da ta’addancin garkuwa da mutane sannan kuma sun raunata dayan.

Sai dai har ya zuwa lokacin tattara wannan rahoto, ASP Sani ya ce basu kama ko mutum day aba amma dai suna ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin.