Wasu fusatattun matasa sun jefe wani direban mota mai shekara 35 da duwatsu har lahira bisa zargin sa da kashe mutum biyu tare da raunata wasu shida a wani hatsarin da ya auku a hanyar Ijoka da ke Akure, babban birnin Jihar Ondo.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Ondo, SP Olufunmilayo Odunlami-Omisanya, ta shaida wa manema labarai cewa hatsarin ya rutsa da wata mota da wani dan acaba..
- ’Yan bindiga sun sace basarake da wasu mutum 13 a Abuja
- NAJERIYA A YAU: Dalilin Da ’Yan Najeriya Ke Gudun Kayayyakin Da Aka Yi A Kasar
Odunlani-Omisanya ta ce, “Hatsarin da ya yi sanadin mutuwar wani dan acaba, amma maimakon mutanen da ke wajen su taimaka, sai suka dauki doka a hannunsu ta hanyar kashe matashin tare da kone motarsa.”
Ta kara da cewa da jami’an tsaro ba su isa wurin a kan lokaci da abin ya fi haka muni domin matasan sunyi kokarin kashe iyayen direban wadanda suka zo wajen da lamarin ya auku ne don ganin abin da ke faruwa.
“An tabbatar da mutuwar mutum biyu yayin da wasu shidan suka samu rauni a hatsarin, a halin yanzu suna samun kulawa a asibiti,” in ji ta.
Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), ya ruwaito cewa ana zargin direban motar ya yi tukin ganganci ne inda ya yi awon gaba da wasu ’yan acaba kusan biyar dauke da fasinjoji a yankin Ijo Mimo.
Wani ganau da ya bukaci a boye sunansa, ya ce mutum uku ne suka mutu nan take, wasu kuma suka samu raunuka daban-daban.
“Direban motar, wanda bai samu wani rauni ba, yana kokarin tserewa daga wurin, kafin wasu matasa suka kama shi, suka lakada masa dukan,” in ji shi.
Ya kara da cewa wadanda suka samu raunuka an kai su wani asibiti da ke kusa yankin, yayin da aka bar gawar direban a wajen.