’Yan sanda sun fara bincike kan kisan ramuwar gayya da aka yi wa wani mutum nda ake zargi da yi wa wani manomin shinkafa kisan gilla.
Kisan gillar da aka yi wa manonmin mai suna Ngozi Ogbuewu da kisan ramuwar gayyar sun auku ne a yankin Nenwe na Karamar Hukumar Aninri ta Jihar Enugu.
- Direban bas ya mayar da N10m da gwala-gwalai da ya tsinta
- Dan bindigar da ya yi garkuwa da Daliban Afaka ya shiga hannu
Shaidu sun ce Ogbuewu ya je gonarsa da ke kauyen Ugwuokpa da ke Nenwe, kuma wanda ake nzargi ne ya yi masa rakiya a hanyarsa ta komawa gida a kan babur. Wanda ake zargin dan asalin garin Nomeh ne a yankin Nkanu na jihar.
Wani mazaunin yankin da bai so a bayyana sunansa ba ya shaida wa manema labarai cewa Ogbuewu ya je gonar shinkafarsa tare ne da matarsa don neman taki da magungunan kashe kwari.
Ya ce a lokacin da manomin yake komawa gida tare da matar tasa a kan babur sai Ubah ya tare masu hanya, ya ture su, matar ta yi sa’a ta tsere, wanda ake zargin ya yi wa mijin yankan rago da adda.
“Bayan da ya yanke kan mutumin, sai ya boye a cikin jakar taki ya tafi da shi gida tare da babur din mamacin.
“Dubunsa ta cika aka kuma kama shi ne a lokacin da kan ya fado daga cikin buhun takin da ke daure a kan babur, nan take mutanen gari suka yi ca a kansa.
“A lokacin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa ya kashe manomin ne saboda sun samu sabani.
“Nan take wasu fusatattun matasa suka yi masa kamun kazar kuku, suka kashe shi suka kuma banka wa gawarsa wuta, bayan sun fatattaki ’yan sandan da suka isa wajen domin shiga tsakani.”
Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Enugu, ASP Daniel Ndukwe, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce Rundunar tana bincike kan abin da ya faru.