Wasu masu zanga-zanga sun yi wa wasu muhimman wurare tsinke a Abuja, ciki har da hedkwatar Babban Bankin Najeriya (CBN), don nuna goyon bayansu ga shirin canza kudi na Gwamnatin Tarayya.
Mutanen, wadanda ke karkashin inuwar Pro-Nigeria, sun kuma fantsama a dandalin Unity Fountain, dauke da kwalayen da ke nuna goyon bayan manufar.
- Canjin kudi: Emefiele ya yaudari Buhari —Oshiomhole
- Kotun Koli ta halasta wa Ahmed Lawan takarar Sanatan Yobe ta Arewa
Batun canjin kudin dai da kuma karancin takardun sabbin kudin da ake samu ya jefa ’yan Najeriya da dama cikin tsaka mai wuya, yayin da wasu ’yan siyasa suke zargin da biyu aka yi.
Wasu daga cikin rubuce-rubucen da ke jikin kwalayen sun hada da; “Mai neman sayen kuri’u ne ba sa goyon bayan CBN”, “A tona musu asiri mai girma Shugaban Kasa”, “Mun yi amanna da Najeriya”, “’Yan Najeriya na kwarai na goyon bayan CBN kan canjin kudi”, “A fallasa masu boye kudi”, da sauransu.
Da yake yi wa manema labarai jawabi, jagoran masu zanga-zangar, Isaac Balami, ya ce sun yanke shawarar goyon bayan manufar ce saboda tana da amfani ga tattalin arziki.
“Mun taru a nan ne a matsayinmu na ’yan Najeriyar da suka san ya-kamata, ba ’yan siyasa ba. Mun taru ne don tattauna manufar CBN kan canjin kudi.
“CBN ya ba da karin kwana 10, amma wasu ’yan siyasar a kasar nan na kokarin siyasantar da lamarin da kuma shafa wa CBN da Shugaban Kasa kashin kaji.
“Wannan manufar ta CBN za ta hana sayen kuri’u. Matsalar sayen kuri’u ta dade tana ci wa Najeriya tuwa a kwarya, lokaci ya yi da za mu ga bayanta,” in ji Isaac Balami.
Zanga-zangar tasu dai na zuwa ne a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke ci gaba da kokawa kan wahalar da karacin takardun kudin ke haifarwa a fadin kasar.