Salam. Abin takaici ga ’yan’uwana matasa musamman masu amfani da kafafen sadarwa na zamani. Bamu da aiki a kullum sai ci wa junanmu mutunci da nufin kare muradun iyayen gidanmu a siyasa. Zagi da cin mutuncin iyayenmu masu daraja ya zamo kamar wani abin azo-a-ni saboda kawai dadadawa wadanda ba mu ne a gabansu ba. Gaba daya mun manta da ‘yancin mu, mun biye wa wadanda ‘ya’yansu da son tara musu kazamar dukiya don kada su tagayyara ne a gabansu. Sun tura’ya’yansu makarantu domin sama musu ingantacciyar rayuwa, mu sun bar mu da duhun kai da tsabagen jahilci da kyamatar juna ba gaira ba dalili. Shin mun taba tsayawa mun yi tunanin me ya sa kullum muke cikin kaskanci a wannan kasa? Kuma mene ne mafita? Babu shakka daya daga cikin dalilan da ya sa kullum muke cikin wahala shi ne kwadayi da son kare wadanda matsayinsu bai kai a kare su ba. Mu tsaya mu yi tunani mu hararo rukuni rukuni na masu mulkar mu, abokai ne su a dukkanin jam’iyyun kasar nan, a koda yaushe sune ke yawo da hankularmu amma saboda gidadanci mun kasa gano hakan. Suna amfani da kaskancin da muka gadar wa kanmu, su mulke mu, diyansu ma su taso su musguna mana. Idan suka tara mu za su nuna mana su da wane sai kisa, amma kuma sau nawa muka gansu tare cikin fara’a da walwala? Hakika idan ba mu farga mun daina cin mutuncin juna ba, mun kuma fitar da kwadayi da son rai, wallahi kaskanci yanzu ma muka fara ganinsa. Allah Ya ganar da mu, Ya sanya mana kaunar juna, Ya kuma azurta mu da zaman lafiya mai dorewa. Allah Ya azurta mu da shuwagabanni masu kaunar mu da gaske.
Sako daga dan uwanku Kabiru Maigari Gumel 08028480098.